Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYadda gwamnatin Zamfara ke shirin tallafa wa mata da ’yan mata sama...

Yadda gwamnatin Zamfara ke shirin tallafa wa mata da ’yan mata sama da miliyan ɗaya

Dauda Lawal ya sake jaddada kudirinsa na tallafa wa mata da masu buƙata ta musamman domin inganta rayuwarsu da tattalin arzikinsu.

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta tabbatar da shirinta na aiwatar da Shirin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Mata (WEE), wanda ake sa ran zai taimaka wa mata da ’yan mata sama da miliyan ɗaya, ciki har da masu nakasa da sauran marasa galihu a jihar.

A wani taron bita na kwanaki uku da aka gudanar a Sokoto, Kwamishinar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma, Dokta Aisha M.Z. Anka, ta bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da bullo da tsare-tsaren da za su ƙara bai wa mata damar samun ilimi, dogaro da kai da kuma shiga harkokin tattalin arziki.

Ta hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Garba Aliyu Gayari, kwamishinar ta ce inganta ilimin mata, kare haƙƙoƙinsu da kuma ba su damar shiga tsarin kuɗi zai taimaka wajen bunƙasa walwalar iyalai da ci gaban al’umma baki ɗaya.

Hakazalika, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya da sauran ƙungiyoyin ci gaba da su ƙara ba da gudunmawa wajen tallafa wa mata a Zamfara domin samun ci gaba a fannoni na zamantakewa, siyasa da tattalin arziki.

Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun gabatar da shawarwari da nufin samar da ingantacciyar manufa da za ta taimaka wajen magance ƙalubalen da mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu ke fuskanta a jihar.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments