Dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare da ceto mutane 31 da aka sace a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Zamfara da Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun gudanar da hare-hare kan maboyar ‘yan bindiga a yankunan da ke Anka, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutum 31 da aka yi garkuwa da su bayan sun shafe makonni a hannun masu garkuwar.
An ce waɗanda aka ceto sun fito ne daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar Zamfara da Sokoto, kuma an ba su kulawar lafiya kafin a mayar da su ga iyalansu.
A wani samame daban a Zamfara, sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da lalata sansanoninsu, sannan suka ƙwato wasu bindigogi da babura da ake amfani da su wajen aikata laifuka.
Haka kuma a jihar Katsina, dakarun soji sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da ake zargin suna shirin kai hari a yankin Matazu, inda suka kashe mutum uku tare da ƙwato babura da harsasai.
Jami’an soja sun bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin kawar da ‘yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Yamma.