Taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar ADC karo na 101 da aka gudanar a Abuja ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, a matsayin wanda ke fuskantar matsin lambar siyasa.
A sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, an ce mambobin kwamitin sun amince baki daya cewa ana yi wa El-Rufai tsangwama saboda dalilan siyasa, don haka suka yi kira da a sake shi cikin gaggawa.
Baya ga haka, kwamitin ya amince da sakamakon zabukan fidda gwani na jam’iyyar na kujerun majalisun jihohi, majalisar wakilai, majalisar dattawa, gwamnoni da kuma shugaban kasa, sai dai a wuraren da ake ci gaba da sauraron korafe-korafe ko kuma ba a kammala tsarin zaben ba.