Shugaban sashen kula da lafiya na Babban Asibitin New Bussa da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja, Dr. Tony Eghagagara, na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane har tsawon kwanaki 33 bayan sace shi, duk da cewa an biya kuɗin fansa har Naira miliyan 20.
An sace likitan ne a ranar 22 ga Afrilu, 2026, a asibitinsa mai zaman kansa da ke wajen garin Wawa a Borgu, inda ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai harin.
Majiyoyi kusa da iyalansa sun shaida wa Daily Trust cewa masu garkuwar sun daina tuntubar iyalai da abokan aikinsa bayan karɓar kuɗin fansar.
Wata majiya ta kuma bayyana cewa ana zargin masu garkuwar na tilasta wa likitan kula da ‘yan kungiyar su da suka jikkata.
Ƙungiyar likitocin gwamnati ta MAGGMDP ta yi kira ga gwamnatin jihar Neja da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da sakin likitan.
A wata sanarwa bayan taron gaggawa, shugaban ƙungiyar, Dr. Mustapha Mohammed Aliyu, tare da babban sakataren ƙungiyar, Dr. Musa Alhaji Shehu, sun nuna damuwa kan tsawon lokacin da likitan ya shafe a tsare.
Ƙungiyar ta kuma koka kan ƙarancin tsaro a cibiyoyin lafiya musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro, duk da yawan kiraye-kirayen da ake yi na kare ma’aikatan lafiya.
MAGGMDP ta buƙaci gwamnati da ta ƙarfafa tsaro a asibitoci da cibiyoyin lafiya, musamman a yankunan karkara da ke yawan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.