Rundunar sojin Najeriya ta gargadi mazauna yankin Arewa maso Gabas da su guji wuraren da ake samun cunkoso yayin bukukuwan Eid El Kabir sakamakon ƙarin fargabar tsaro da ake fuskanta a yankin.
Sojojin sun kuma buƙaci jama’a su kasance cikin shiri tare da bin umarnin jami’an tsaro a duk lokacin bukukuwan, sannan su gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi ko abu da ke tayar da hankali domin dakile yiwuwar hare-hare.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, rundunar ta bayyana cewa an riga an ɗauki tsauraran matakan tsaro kafin fara bukukuwan Sallah.
Sanarwar ta ce an baza jami’an tsaro zuwa wurare masu muhimmanci da kuma waɗanda ake ganin suna cikin haɗari a dukkan sassan yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Rundunar ta ƙara da cewa an ƙarfafa aikin sintiri tare da amfani da kayan sa ido da tattara bayanan sirri domin bibiyar duk wani motsi da zai iya zama barazana.
Haka kuma jami’an tsaro na aiki tare da sauran hukumomin tsaro, da ƙungiyar CJTF da kuma kungiyoyin sa-kai na al’umma domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan.
Sojojin sun shawarci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah a cikin unguwanninsu tare da kauce wa shiga wuraren da ake samun cunkoso ba tare da wata buƙata ba.
An kuma bukaci mutane su gudanar da sallar Idi da sauran bukukuwa kusa da gidajensu maimakon taruwa a manyan wuraren da jama’a ke cika.
Rundunar ta ce jama’a su ƙara sanya ido musamman a kasuwanni, tashoshin mota, bankuna da filayen Idi, tare da kai rahoton duk wani mutum ko abu da ake zargi ga jami’an tsaro nan take.
Laftanar Kanar Uba ya bayyana cewa bayanan sirri da hukumomin tsaro suka samu sun nuna yiwuwar ragowar mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na iya ƙoƙarin kai hare-hare yayin bukukuwan Sallah.
Ya ce ana zargin maharan na iya amfani da ‘yan kunar bakin wake ko kuma bama-bamai da aka haɗa cikin sirri domin kai hare-hare musamman a wuraren da jama’a ke taruwa da yawa.
Sai dai rundunar ta tabbatar wa al’umma cewa jami’an tsaro sun riga sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana da ka iya tasowa.
Sojojin sun kuma roƙi sarakunan gargajiya, malaman addini, kafafen yaɗa labarai da shugabannin al’umma da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin kai bayanan sirri cikin gaggawa.
Rundunar ta jaddada cewa dakarunta na cikin shiri domin hana ‘yan ta’adda samun damar kawo cikas ga bukukuwan Sallah a yankin.