Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHisbah ta kama matar aure a samamen da kai otal a jihar...

Hisbah ta kama matar aure a samamen da kai otal a jihar Kebbi

Jami’an Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi, sun kama wata matar aure tare da wasu mutane biyar a wani samamen da suka kai wasu otal-otal bisa zargin aikata baɗala.

Jami’an Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi, sun kama wata matar aure tare da wasu mutane biyar a wani samamen da suka kai wasu otal-otal bisa zargin aikata baɗala.

Daraktan hukumar, Surajo Usman, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne a wasu otal da ke Birnin Kebbi da Makera, inda aka kama mutanen suna aikata abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’a da koyarwar addini.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kama har da wata matar aure mai ‘ya’ya huɗu, lamarin da ya tayar da hankali a tsakanin jami’an hukumar. Ya yi kira ga al’umma da su ji tsoron Allah, su kiyaye mutuncin aure, kuma su guji duk wani aiki da zai iya kawo fitina da rashin zaman lafiya a cikin al’umma.

Hukumar ta ce a yayin samamen, ta kuma ceci wasu yara biyu da suka ɓata, inda aka mayar da su hannun iyayensu lafiya. Haka kuma, an gano wata mata mai matsalar tabin hankali daga Zuru wadda ta ɓace tsawon shekaru uku, kuma an haɗa ta da iyalanta.

A wani lamari daban, hukumar ta taimaka wajen sasanta rikicin aure da dama, ciki har da wata mata daga Gombe da ke fama da matsalar aure da mijinta da ke Jamhuriyar Nijar, inda aka mayar da ita ga iyayenta bisa buƙatarsu.

Daraktan ya yi gargaɗi ga duk masu aikata irin waɗannan abubuwa da su tuba su daina, yana mai cewa duk wanda aka sake kama da irin wannan hali zai fuskanci hukunci mai tsauri ba tare da sassauci ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments