Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiRundunar 'yan sanda ta fara tankade da rairaya, an kori jami'ai masu...

Rundunar ‘yan sanda ta fara tankade da rairaya, an kori jami’ai masu garkuwa da mutane da fashi

Rundunar ta ce jami’an sun ci amanar ƙa’idoji da martabar aikin ɗan sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori tare da kama wasu jami’anta da ake zargi da hannu a laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, karɓar cin hanci, sata da kuma amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba a jihar Rivers.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Anthony Okon Placid ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a shafin Facebook na rundunar a ranar Alhamis, rundunar ta ce ayyukan jami’an da abin ya shafa babban cin amana ne ga ɗabi’u, ƙa’idoji da martabar aikin rundunar ‘yan Sandan Najeriya.”

Shugabancin rundunar ƙarƙashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya ce ya kuduri aniyar gano, tona asiri tare da kawar da masu aikata laifi daga cikin rundunar, ba tare da la’akari da matsayi ko muƙami ba.

Sanarwar ta ce bincike ya gano wata ƙungiyar masu aikata laifi da ta haɗa da jami’an ‘yan sanda masu aiki a hedikwatar Zone 16 da ke Yenagoa. Jami’an da aka ambata sun haɗa da sufetoci Ayanniyi Jelili, Durojaye Francis da Olayemi Titus.

Rundunar ta yi zargin cewa jami’an sun shiga ayyukan fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma karɓar kuɗin fitina yayin gudanar da sintiri ba bisa ƙa’ida ba a Port Harcourt.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an suna sace mutane yayin binciken ababen hawa da suka saba doka, sannan su tilasta musu buɗe manhajojin banki da na kuɗin crypto domin karɓar kuɗi

‘Yan sanda sun ce wasu abokan aikinsu guda uku — Sufeto Awele Ogbogu, Sufeto Prosper Aghotor da Koporal Favour Onwuchekwa — har yanzu ana nemansu ruwa a jallo.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da motocin Toyota Sienna guda uku da ake zargin an yi amfani da su wajen ayyukan, da kuma kuɗi har Naira miliyan 7,338,800 da aka danganta da ayyukan laifin.

A wani binciken daban, rundunar ta ce ta gano wata ƙungiyar masu aikata laifi da ta haɗa da jami’an da a baya suke aiki a Sashen Ayyuka na Rundunar Rivers. Jami’an sun haɗa da Sufeto John Okoi, Sufeto Eyibo Asuquo, Sufeto Udo Ndipmong, Sufeto Bright Nwachukwu da Sufeto Anele Ikechukwu.

Sanarwar ta ce: “Jami’an sun shiga shirya ayyukan garkuwa da mutane, karɓar kuɗin cin hanci da sata yayin da suke fakewa da aikin sintiri.”

Rundunar ta ƙara da cewa an kori jami’an biyar bayan kammala binciken cikin gida, sannan an miƙa fayil ɗin shari’arsu domin gurfanar da su kan tuhume-tuhumen haɗa baki, fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuffukan.

Har ila yau, rundunar ta buƙaci jama’a su ci gaba da kai rahoton cin zarafi, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

“Rundunar yan sandan Najeriya na nan daram wajen tabbatar da aikin ‘yan sanda bisa ƙwarewa, gaskiya, riƙon amana da kuma kare haƙƙin jama’a bisa tanadin doka,” in ji sanarwar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments