Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAPC ta yaba wa Ahmed Lawan da sauran ƴan siyasa da suka...

APC ta yaba wa Ahmed Lawan da sauran ƴan siyasa da suka janye daga takarar gwamnan Yobe

Jam’iyyar APC a jihar Yobe ta yaba wa wasu manyan ‘yan takarar gwamna da suka janye daga takarar gwamna domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Jam’iyyar APC a jihar Yobe ta yaba wa wasu manyan ‘yan takarar gwamna da suka janye daga takarar gwamna domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ta yabawa musamman tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da wasu ‘yan takara bisa matakin da suka ɗauka na janyewa daga takarar.

Shugabannin APC sun bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage rikice-rikice da ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar a jihar Yobe. Sun kuma ce hakan na nuna kishin jam’iyya da fifita muradun al’umma fiye da anfani na kai.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa janyewar ‘yan takarar zai bai wa APC damar shiga zaɓe cikin ƙarfi da haɗin kai, musamman ganin yadda ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓukan 2027.

Haka kuma, APC ta yi kira ga sauran mambobi da magoya baya da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya tare da gujewa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kai a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments