Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta yanke wa limamin coci ɗaurin rai da rai bisa laifin...

Kotu ta yanke wa limamin coci ɗaurin rai da rai bisa laifin fyade

Wata babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ta yanke wa babban limamin cocin Mission Prophet Ajiboye Abayomi Olayinka, hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samunsa da laifin yi wa ƙananan yara mata uku fyade a cikin harabar cocin.

Wata babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ta yanke wa babban limamin cocin Mission Prophet Ajiboye Abayomi Olayinka, hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samunsa da laifin yi wa ƙananan yara mata uku fyade a cikin harabar cocin.

Kotun ta same shi da laifuka uku daban-daban na yin lalata da yara ‘yan shekara 13, lamarin da ya faru a gidan mishan na cocin da ke yankin Agah a Ganmo, inda yake jagorantar cocin.

Haka kuma, kotun ta ƙara yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 14 saboda zargin zubar da cikin wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ba bisa ƙa’ida ba, tare da yi musu barazanar kada su tona asirin abin da ya aikata.

Mai shari’a Hammed Aliyu Gegele ya bayyana cewa limamin ya yi amfani da matsayinsa na malamin addini wajen cutar da yaran ta fuskar jima’i da kuma tunani.

Kotun ta bayyana cewa ɗaya daga cikin yaran ta shaida yadda limamin ya kai ta ɗakin janareta inda ya tilasta mata yin jima’i da shi.

An gurfanar da limamin ne bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, lalata da ƙananan yara, zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba da kuma mallakar bindiga ba bisa doka ba.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu guda 12 tare da wasu hujjoji a gaban kotu.
Yaran da abin ya shafa sun bayyana cewa limamin yana sa su yin rantsuwa da Littafi Mai Tsarki kan ba za su bayyana abin da ya aikata ba, yana musu barazanar mutuwa idan suka faɗa wa kowa.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Gegele ya ce an tabbatar da laifukan fyade da lalata da yara da kuma zubar da ciki a kan wanda ake tuhuma, amma ba a samu isasshiyar hujja kan zargin auren mata fiye da ɗaya ba, saboda haka aka wanke shi daga wannan tuhuma.

Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace bindigar pump-action da aka samu a hannunsa domin miƙa ta ga gwamnatin tarayya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments