Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bai ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, kuma bai mara wa kowane ɗan takara baya ba, yana mai cewa duk jita-jitar da ake yadawa ba su da tushe kuma sun yi wuri.
Jita-jitar ta fara ne bayan taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, inda aka riƙa danganta shi da yiwuwar haɗa tikitin takara da Peter Obi.
Lamarin ya ƙara ƙamari yayin da magoya bayan su ke yaɗa fastocin yaƙin neman zaɓe a kafafen sada zumunta, tare da rahotannin cewa suna shirin ficewa daga ADC zuwa NDC.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya musanta rahotannin.
Ya ce:
“Ina so in bayyana cewa ba a yanke wani hukunci na ƙarshe ba dangane da makomar siyasa ta ko ta abokan hulɗana ba.”
Ya ƙara da cewa har yanzu ADC ba ta yanke shawara kan tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ba.
“Saboda haka ban ayyana tsayawa takara ba, kuma ban mara wa kowane ɗan takara baya ba,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma yi magana kan rikicin cikin gida na jam’iyyar bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, yana mai cewa hakan ya jefa ADC cikin halin ni ƴa su.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da tuntuba da bangarori daban-daban na siyasa, ciki har da NDC da wasu, domin nemo mafita, tare da alƙawarin cewa za su sanar da matsayarsu nan ba da jimawa ba.