Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiCELOHA, WAN sun bukaci gwamnatin jihar Kano ta hanzarta kafa kwamitin kare...

CELOHA, WAN sun bukaci gwamnatin jihar Kano ta hanzarta kafa kwamitin kare yara

Ƙungiyoyin sun ce rayuwar yara na fuskantar haɗari, saboda haka akwai buƙatar matakin gaggawa

Cibiyar CELOHA Nigeria tare da hadin gwiwar West Africa Network for Child Protection (WAN) sun bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta kaddamar da Kwamitin kan kare raya.

Kungiyoyin sun gargadi cewa jinkirin na jefa yara cikin hadari tare da raunana kokarin kare su.

A cikin sanarwar hadin gwiwa, sun ce, “ci gaba da jinkiri na jefa rayuwa, mutunci, da makomar dubban yara cikin hadari mai tsanani.

”Sun bayyana cewa rashin wannan muhimmin kwamitin hadin kai ya haifar da babban gibi a tsarin kare yara, wanda ke barin yara cikin hadarin fataucin yara, aikin yara, bara a titi (matsalolin Almajirai), cin zarafi, sakaci, auren wuri/tilas, da kuma hijira.”

Sanarwar ta kara da cewa, “rashin wannan muhimmin tsarin hadin kai ya haifar da gibi mai yawa a tsarin kare yara.

Kungiyoyin sun ce ana samun jinkiri ko kuma rashin bayar da rahoton cin zarafi, yayin da wadanda abin ya shafa ke fama da rashin samun kulawa, gyara da dawo da su cikin al’umma a kan lokaci.

Sun kuma lura da raunin aiwatar da dokoki da rashin isassun bayanai don tsara tsare-tsare.

Sun jaddada muhimmancin kwamitin wajen hada kai tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula da abokan hulda, da kuma inganta daukar mataki cikin gaggawa kan batutuwan kare yara.

Sun ce, “CELOHA Nigeria da WAN sun jaddada cewa Kano, duba da yawan al’umma da muhimmancinta, na bukatar tsari mai karfi, hadin kai da kuma saurin daukar mataki wajen kare yara da matasa daga kalubale.”

Sun yabawa kokarin da gwamnati ke yi, amma suka gargadi cewa jinkiri na rage tasirin wadannan kokari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments