Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa dakarun rundunar soji ta 17 Brigade sun hallaka wasu mutane hudu da ake zargin ƴan ta’adda ne a yayin sintiri kan hanyar Turare zuwa Ƴan Tumaki.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta fitar a ranar Asabar, an ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na safe a ranar Juma’a, lokacin da dakarun suka fuskanci harin ‘yan bindiga.
Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fi ƙarfin maharan tare da kashe su baki ɗaya ba tare da sun yi asarar rai ba.
Jami’an tsaro sun kwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya tare da ƙunshin harsashi mai ɗauke da harsasai biyar, babura biyu, wayoyin hannu da dama, da kuɗi har naira 153,400.
Hukumomi sun bayyana cewa wasu daga cikin wayoyin Android ɗin da aka kwato na ɗauke da hotunan waɗanda ake zargin sanye da kayan soji, kuma an miƙa su domin binciken kimiyya.
Binciken farko ya gano sunayen waɗanda aka kashe da suka haɗa da Bishir Holami, Jamilu Baki, Ibrahim Doro, da Abdurraman Maje.
Gwamnatin ta bayyana su a matsayin manyan jagororin hare-haren da suka addabi yankunan Gobirawa, Raddawa, Kuki da sauran al’ummomi a ƙananan hukumomin Dutsinma da Matazu.
Haka kuma jami’ai sun ce kashe su babbar illa ce ga wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Muhammadu Fulani, wanda ake danganta shi da hare-hare a yankunan Matazu, Musawa, Charanchi da Kankia.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Dakta Nasir Mu’azu, ya ce wannan nasara na nuna ƙudirin gwamnan jihar Dikko Umaru Radda wajen magance matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya.
Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan masu aikata laifi.
Ya buƙaci al’umma su kasance masu lura tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, yana mai cewa bayanan sirri daga jama’a sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da aka samu a baya-bayan nan.