Wasu ‘yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda a ƙauyen Tenebo, ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda suka kashe akalla jami’ai uku tare da jikkata wasu biyu.
Harin, wanda ya faru da sanyin safiyar Asabar, ya zo wa jami’an tsaron a bazata.
An ce maharan sun shigo wurin da yawa, wasu daga cikinsu suna kan babura.
Wani mazaunin yankin, Malam Mohammed Abdul, ya ce:
“Sun zo wajen karfe 2 na dare da yawa, suka yi ƙoƙarin shiga gari amma jami’an tsaro suka tare su, wanda hakan ya jawo musayar wuta mai tsawo da ta ɗauki sa’o’i.”
Ya ƙara da cewa:
“A ƙarshe, jami’ai uku sun mutu, biyu kuma sun jikkata. ‘Yan bindigar sun tafi daga baya, amma ba a yi garkuwa da kowa ba, kuma ba mu san ko an kashe wasu daga cikinsu ba.”
Wani mazaunin, Malam Halidu Umar, ya ce:
“Babu wanda ya samu bacci a daren, har yanzu muna cikin tsoro saboda ƙauyen Tenebo yana da kusan kilomita 4 daga garin Kaiama.”
Ya ƙara da cewa:
“Ƙauyen Tenebo yana kaiwa zuwa Gandun Dajin Ƙasa, National Park, inda ake zargin ‘yan bindigar ke fakewa. Wannan hari ya yi kama da wasu hare-haren da suke kaiwa su kuma gudu zuwa cikin daji.”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin a wata hira ta waya da aka yi da shi.
Ya ce:
“Eh gaskiya ne, mun rasa jami’ai uku jarumai a harin, yayin da biyu suka jikkata.
Wadanda suka
jikkata suna samun kulawa, amma ba a kama kowa ba har yanzu.”
A watan da ya gabata, an samu irin wannan hari inda ‘yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin gwiwar jami’an tsaro a Kemanji, wani ƙauye kusa da Tenebo, inda suka kashe sojoji uku da ‘yan sa-kai biyu.
Haka kuma, sun kwashe wata motar soji mai dauke da bindigogi da sauran kayan aiki, duk da cewa an ce sun yi asara a nasu bangaren.
Tun da farko ma, ‘yan bindiga sun kashe mutum biyar daga cikin masu tsaron daji a ƙauyen Nuku, sannan suka ƙone motocinsu da wuraren aikinsu.