Gwamnatin tarayya ta ware fiye da Naira biliyan 5 domin tallafawa ilimi a matakin farko, a wani mataki na dakile matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Kazalika shirin na da manufar inganta tsarin makarantu, da karfafawa alumma, da kuma ci-gaba da sanya raya makarantu a fadin kasar nan.
Shirin da hukumar ilimin bai-daya ta kasa, UBEC ke gudanarwa karkashin shirin kula da makarantu, ya soma ne an Abuja a wani bangare na ayyukan da za ta gudanar a shekarar 2025.