Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamna Bago ya bada umarnin gyaran gine-ginen da suka lalace a sansanin...

Gwamna Bago ya bada umarnin gyaran gine-ginen da suka lalace a sansanin NYSC

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da umarnin a gyara gine-ginen da guguwar iska ta lalata a sansanin horo na NYSC da ke Paiko, a ƙaramar hukumar Paikoro ta jihar.

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da umarnin a gyara gine-ginen da guguwar iska ta lalata a sansanin horo na NYSC da ke Paiko, a ƙaramar hukumar Paikoro ta jihar.

Bago ya bayar da wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bologi Ibrahim, ya fitar a daren Lahadi a Minna.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da damuwa, yana mai cewa ya jefa ‘yan bautar ƙasa da ma’aikatan sansanin cikin wani hali mai wahala.

Gwamnan ya ce gyaran gaggawa na gine-ginen da suka lalace zai taimaka wajen rage matsalar tare da bai wa sansanin damar ci gaba da gudanar da horo cikin sauƙi.

Ya kuma yaba wa tawagar da ta je duba lalacewar, wacce ta haɗa da jami’an gwamnati na jihar, Darakta Janar na NYSC, Brigediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, da kuma Kwamishinan NYSC na jihar, Martina Shuaibu-Ibrahim, bisa haɗin kai da suka yi wajen samar da ɗakunan karatu a wata makarantar sakandare da ke kusa domin amfani na wucin gadi.

Bago ya sake jaddada goyon bayansa ga NYSC domin tabbatar da tsaro da walwalar dukkan masu yi wa ƙasa hidima a jihar.

Daga cikin gine-ginen da guguwar ta lalata akwai ɗakunan kwanan ‘yan bautar ƙasa maza, babban ɗakin taro, ɗakin girki, gidajen ma’aikata, da wasu sassan gidan kwamishinan NYSC na jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments