Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBabbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta ƙaddamar da tsarin shigar da...

Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta ƙaddamar da tsarin shigar da ƙara ta yanar gizo

Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta ƙaddamar da tsarin shigar da ƙara ta yanar gizo da ake kira da E-Filing a turance, a reshen ta na jihar Legas, wanda ke nuna babban sauyi daga tsarin amfani da takardu zuwa na zamani, domin ƙara inganci, gaskiya da kuma riƙon amana a harkar shari’a.

Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta ƙaddamar da tsarin shigar da ƙara ta yanar gizo da ake kira da E-Filing a turance, a reshen ta na jihar Legas, wanda ke nuna babban sauyi daga tsarin amfani da takardu zuwa na zamani, domin ƙara inganci, gaskiya da kuma riƙon amana a harkar shari’a.

Babban Alkalin kotun, John Terhemba Tsoho, wanda ya ƙaddamar da tsarin a ranar Litinin, ya bayyana cewa zamanin amfani da takardu wajen shigar da ƙara a kotun ya zo ƙarshe.

Ya ce sabon tsarin zai kawar da matsalolin da aka saba fuskanta a tsohon tsarin, kamar jinkiri, canza ranakun takardu, da kuma ayyukan wasu mutane marasa izini a cikin ofishin rajista.

Tsoho ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabon tsarin, ana iya shigar da ƙara a kowane lokaci daga ko’ina, domin ba za a ƙara takaita aikin rajista da lokutan rufewa ba.

A cewarsa, tsarin ya kuma kawo bin diddigin shari’o’i kai tsaye, tare da haɗa hanyoyin biyan kuɗin kotu ta yanar gizo domin tabbatar da cikakkiyar gaskiya da riƙon amana.

Babban alkalin ya ƙara da cewa lokacin da ake ɗauka kafin takardun shari’a su isa ga alkali zai ragu sosai “daga kwanaki zuwa sakan kaɗan,” wanda ake sa ran zai hanzarta gudanar da shari’a.

Ya ce wannan shiri ya yi daidai da umarnin Babbar Alkalin Najeriya, Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun, wacce ta jaddada muhimmancin amfani da fasaha a bangaren shari’a.

Yayin da ya ƙarfafa lauyoyi su fara amfani da sa hannu da tsarin rantsuwa na yanar gizo, Tsoho ya ce har yanzu za a ci gaba da buƙatar takardu na asali a halin yanzu, har sai an kammala komawa gaba ɗaya zuwa tsarin mara takarda.

Ya amince cewa za a iya fuskantar wasu ƙalubale a farko, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa tsarin zai inganta ayyukan kotu tare da ƙara amincewar jama’a ga tsarin shari’a.

Ƙaddamar da wannan tsarin na nuni da wani babban mataki na sabunta tsarin kotunan Najeriya da kuma yunƙurin komawa ga tsarin shari’a na zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments