Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiINEC ta wanke shugabanta daga zargin mallakar shafin X

INEC ta wanke shugabanta daga zargin mallakar shafin X

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta wanke shugabanta, Farfesa Joash Ojo Amupitan, daga zarge-zargen da ake yi masa, yayin da matsin lamba ke ƙaruwa daga jama’a da ƙungiyoyi suna buƙatar ya sauka daga muƙaminsa.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta wanke shugabanta, Farfesa Joash Ojo Amupitan, daga zarge-zargen da ake yi masa, yayin da matsin lamba ke ƙaruwa daga jama’a da ƙungiyoyi suna buƙatar ya sauka daga muƙaminsa.

Ana ci gaba da kiraye-kirayen murabus ɗinsa ne bayan yaɗuwar wasu saƙonni a kafar X da ake zargin suna nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu. Wannan lamari ya sa wasu ƙungiyoyin farar hula da masu sa ido kan zaɓe suka nuna damuwa cewa hakan na iya rage amincewar jama’a da hukumar kafin zaɓen 2027.

’Yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da matasan jam’iyyar ADC sun shiga cikin masu kira da ya sauka, inda suka gudanar da zanga-zanga a ofishin INEC da ke Legas da kuma gaban majalisar dokokin Birtaniya.

Haka kuma wata ƙungiyar farar hula mai suna Movement for Credible Elections, MCE, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Pat Utomi tare da wasu manyan mutane, ta buƙaci Amupitan ya ajiye aiki domin a gudanar da bincike na gaskiya kan zarge-zargen.

Sai dai INEC ta bayyana cewa wani bincike na fasaha, forensic investigation da aka gudanar bai samu wata shaida da ke danganta shugaban hukumar da asusun X ɗin ba. Hukumar ta ce dukkan saƙonnin da ake danganta masa na ƙarya ne, kuma wani shiri ne na yaɗa bayanan bogi domin yaudarar jama’a.

A cewar INEC, binciken ya gano wasu abubuwa da ke nuna cewa an ƙirƙiri asusun ne ta hanyar amfani da fasahar zamani ta AI, ciki har da wani lokaci da aka nuna an yi martani ga saƙo kafin ma a wallafa saƙon na asali, wanda ba zai yiwu ba.

Hukumar ta kuma ce an gano wasu asusun bogi a Facebook da Instagram da ke amfani da sunan Amupitan, wanda ke nuna cewa akwai wani tsari na kwaikwayo da yaɗa ƙarya a kansa.

Duk da haka, mutane da dama sun ƙi amincewa da rahoton binciken na INEC, suna zargin cewa binciken ba ya da cikakkiyar gaskiya.

Wasu daga cikin masu amfani da kafar X sun bayyana cewa bayanan da aka bayar ba su gamsar ba, kuma sun buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa.

Wasu sun nuna damuwa cewa idan ba a magance wannan rikici ba, zai iya shafar amincewar jama’a da zaɓe mai zuwa a shekarar 2027.

A ƙarshe, INEC ta buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai da su riƙa tantance bayanai kafin yaɗawa, tana mai gargadin cewa ci gaban fasaha ya sa ya zama mai sauƙi a ƙirƙiri bayanan bogi masu kama da na gaske.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments