Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance, inda ya bayyana cewa hakan na da nasaba da wani sabon tsarin siyasa da yake shirin bi.
A cikin wasikar murabus mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Afrilu, 2026, da aka aike wa shugaban PDP na mazabar Giginyu a ƙaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano, Shekarau ya bayyana cewa ficewarsa ta fara aiki nan take.
Tsohon ministan ya ce wannan mataki ya biyo bayan shawarwari da tuntuba da suka gudana a siyasarsa, yana mai nuni da cewa suna dab da komawa wata jam’iyya.
“Wannan shawara ta biyo bayan tattaunawa mai faɗi da zurfi a cikin ƙungiyarmu ta siyasa, domin ci gaba da tafiyar da harkokinmu a wata jam’iyya dabam,” in ji Shekarau.
Yayin da ya nuna godiya ga shugabannin jam’iyyar a matakin mazaba, ya ƙara da cewa: “Ina gode maku bisa kyakkyawan jagoranci, kuma ina roƙon Allah ya ci gaba da shiryar da ku a jagorancinku.”
An kuma aika kwafin wasiƙar ga shugaban PDP na jihar Kano da kuma shugaban PDP na ƙaramar hukumar Nassarawa, wanda ke nuna cewa an sanar da dukkan matakan jam’iyyar a hukumance.
Ficewar Shekarau na daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa a jihar Kano, inda sauya sheƙa ke ci gaba da tasiri wajen shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe.