Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKano: Mutane 2 sun mutu, 20 sun jikkata a hatsarin mota

Kano: Mutane 2 sun mutu, 20 sun jikkata a hatsarin mota

Hukumar kiyaye hadura FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum biyu, yayin da wasu 20 suka jikkata, sannan takwas suka tsira ba tare da rauni ba a wani hatsarin mota da ya afku a mahadar Wudil T-Junction da ke kan titin Maiduguri Road a Kano.

Kwamandan hukumar a jihar, Idris Muhammed-Lawan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na FRSC, Abdullahi Labaran, ya fitar ranar Asabar a Kano.

Sanarwar ta ce:
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 9:25 na safe, kuma mun isa wurin cikin mintuna 10.

“Hatsarin ya shafi wata babbar mota kirar DAF dauke da kaya da fasinjoji, wadda ta taso daga kasuwar Wudil tana kan hanyarta ta zuwa Lagos.”

Ta ƙara da cewa, “Dukkanin fasinjojin maza ne manya guda 30 mutum biyu sun rasu, 20 sun samu raunuka iri-iri, yayin da takwas ke nan lafiya.”

A cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa direban ya rasa iko da motar ne sakamakon gudun wuce kima yayin da yake kusantar mahadar T-Junction, inda ya bugi wata mota da ke ajiye a gefen hanya.

An kuma bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Wudil domin samun kulawa.

Sanarwar ta kuma jiyo kwamandan yana nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da karya dokokin kiyaye haɗurra a kan hanya, musamman amfani da manyan motoci wajen ɗaukar fasinjoji.

Ya ce gudun wuce kima da kuma lodin da ya wuce kima na daga cikin manyan musabbabin hatsarin mota, tare da kira ga direbobi da su bi dokokin hanya yadda ya kamata.

Haka kuma, Muhammed-Lawan ya shawarci al’umma da su guji hawa manyan motoci da sauran ababen hawa marasa aminci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments