Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani sarkin gargajiya tare da matarsa da wani mutum guda a wani mummunan hari da suka kai da tsakar dare a unguwar Olayinka da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.
An ce sarkin yana daga cikin wadanda gwamnatin jihar ta kara musu matsayi kwanan nan.
Rahotanni sun nuna cewa maharan, dauke da manyan makamai, sun kutsa cikin fadar sarkin, Oba Salman Aweda, da misalin karfe 1:40 na dare a ranar Asabar, inda suka rika harbe-harbe domin tsoratar da jama’a kafin su yi awon gaba da shi da wasu biyu zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai harin ne a farkon dare.
Wani mazaunin garin shima ya bayyana yadda harin ya kasance cikin sauri da firgici, yana mai cewa babu wanda ya iya tunkarar ‘yan bindigar saboda yadda suka zo dauke da makamai masu yawa. Sarkin Ora, Oba Rilwan Yekini, ya tabbatar da harin, yana mai cewa hakan na nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankunan da ke makwabtaka da su, har ya ce yanzu ma Ora ba ta da cikakken tsaro.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki, yana mai cewa da taimako kaɗan ga jami’an tsaro da masu sa-kai, za a iya samun sauyi cikin kankanin lokaci.
Ya kara da cewa harin ya faru ne kwanaki kadan bayan wani makamancin haka a yankin Odo-Ore, lamarin da ke kara nuna yiwuwar tsari na hare-haren satar mutane a yankin.
Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Hadji Abdulrasheed Yusuf, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, yana mai cewa ana kokarin ceto wadanda aka sace tare da hadin gwiwar jami’an tsaro.
Ya ce an fara gudanar da bincike da sintiri a dazuka da yankunan da ke kewaye, tare da kira ga al’umma da su kwantar da hankula su kuma bayar da bayanan da za su taimaka.
Shi ma kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya ce an kara matsa lamba kan masu aikata laifin, yana mai cewa suna bin diddigin masu hannu a ciki, ciki har da masu taimaka musu daga cikin al’umma.