Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeHormuz: Muna nesa da cimma yarjejeniya da Amurka – Iran

Hormuz: Muna nesa da cimma yarjejeniya da Amurka – Iran

Iran ta nuna cewa har yanzu ana da sauran tazara mai yawa kafin a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka kan Hormuz.

Iran ta bayyana cewa har yanzu tana nesa da cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka, yayin da wa’adin tsagaita wuta na makonni biyu ke gab da ƙarewa ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da aka yada a talabijin ranar Asabar, inda ya ce har yanzu akwai gibi da dama da kuma muhimman batutuwa da ba a warware ba.

“Har yanzu muna nesa da tattaunawar ƙarshe,” in ji Ghalibaf, wanda ya jagoranci tawagar Iran a zagayen farko na tattaunawar da aka gudanar a Islamabad, Pakistan a ranar Asabar din da ta gabata.

A cewarsa, Iran ta samu nasara a fagen fama a cikin makonnin yaƙi, kuma ta amince da tsagaita wuta na wucin gadi da Amurka ne kawai bayan an amince da wasu daga cikin bukatunta.

“Idan muka amince da tsagaita wuta, to saboda sun amince da bukatunmu ne,” in ji shi.

Shugaban majalisar ya ƙara da cewa Amurka ba ta cimma manufofinta ba, yayin da Iran ke da iko kan muhimmiyar mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, wadda ke da matuƙar tasiri a harkokin sufuri na man fetur a duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments