Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaADC ta kori Nafi’u Bala Gombe daga Jam’iyyar sakamakon zagon ƙasa

ADC ta kori Nafi’u Bala Gombe daga Jam’iyyar sakamakon zagon ƙasa

Jam’iyyar adawa ta ADC ta kori tsohon maitaimakin jam’iyyar na ƙasa mai iƙirarin shugabancin Jam’iyyar Nafi’u Bala Gombe da wani mamba na jam’iyyar Leke Abejide.

Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a yayin taronta na ƙasa da ta gudanar.

An kori Nafi’u Gombe ne dalilin “yi wa jam’iyya zagon ƙasa”, kamar yadda Faisal Kabiru ɗaya daga cikin masu magana da jam’iyyar ne ya bayyana hakan, wanda ya jefe jam’iyyar cikin mawuyacin hali.

An kori nafi’u Gombe tare da wasu da suka haɗa da Kenneth Ehiator daga Abia wanda shi ma yake iƙirarin shugabancin jam’iyya a jihar, da Stella Chukwu da kuma Elias Adiukwu.

Nafi’u da ya dage kan zama shugaban jam’iyyar ya fitar da sanarwar waɗanda suka shiga jam’iyyar su Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso ba halastattun ‘yan jam’iyya ba ne, saboda sun shiga ba ta hannunsa ba, kazalika katin ‘yan jam’iyyarsu a shi da wani amfani.

Ya kuma jagoranci zanga-zangar da aka yi an Abuja, wadda ta mayar da hankali wajen neman hukumar zaɓe INEC ta yarda da shi a matsayin halastaccen shugaban ADC.

A babban taron da jam’iyyar ta gudanar na ƙasa, an amince da David Mark a matsayin shugaban ADC na ƙasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare da dai sauransu.
Idan ba a manta ba, a wani taron manema labarai da ADC ta yi ta nemi Shugaban INEC ya sauka da muƙaminsa saboda cire sunan Sanata David Mark daga shugaban jam’iyyar da sauran muƙarrabansa.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments