Tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na shirin kwace mulki daga hannun Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027, tare da karɓe iko a Aso Rock.
Oyegun ya faɗi hakan ne yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a taron ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya nuna cikakken kwarin gwiwa cewa ADC ta shirya tsaf domin jagorantar ƙasa.
Ya ce, “Mun shirya kwace iko a Aso Rock, kuma ba zai zama kamar yadda aka saba ba. Ina so kowa ya sani saboda suna zargin cewa ni na taba kasancewa cikinsu.”
Ya kuma koka kan yadda duk da arzikin da Najeriya ke da shi, har yanzu jama’a na fama da wahalhalu, yana mai cewa hakan gazawar shugabanci ne na tsawon lokaci.
Ya ƙara da cewa shugabannin ADC na kawo sabon fatan da ake na na sauyi, tare da jaddada cewa jam’iyyar na shirin ceto ƙasar daga halin da take ciki.
Oyegun ya yi alƙawarin cewa idan ADC ta hau mulki, za ta ba da muhimmanci ga gaskiya da riƙon amana, tare da hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba a ofis.
A nasa ɓangaren, sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya soki gwamnatin Tinubu, yana mai cewa shirin “Renewed Hope” da take yi “yaudara ce”, domin yawancin alƙawuran da aka yi ba su cika ba har yanzu.