Rundunar sojin Amruka ta ce matakin haramta zirga-zirga a dukan tashoshin ruwan Iran zai fara aiki daga yammacin wannan litinin.
Rundunar ta ce matakin haramta zirga-zirga a dukkan tashoshin ruwan Iran za ta fara aiki daga yammacin wannan litinin 13, Afrilu, 2026.
Cibiyar tsara ayyukan sojin Amruka a yankin Gabas ta Tsakiya CENTCOM , ta rubuta a shafinta na X da yammacin jiya lahadi cewa takun-kumin hana zirga -zirga jirage a dukan tashoshin ruwan Iran a mashigin ruwan Hormuz zai fara aiki da tsakar ranar 13 ga wanan watan bayan tattunawa sulhu da suka gudanar ranar asabar a Pakistan ta kasa haifar da da mai ido.
Sanarwa ta kara da cewa matakin zai shafi dukan jiragen ruwa da ke shiga da a fita a gabobin ruwan ciki har da na Fasha da kuma Oman.