Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiIran ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin soji da...

Iran ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin soji da ya yi yunƙurin shiga mashigar Hormuz

Iran ta jaddada cewa duk wani yunƙuri na shiga Strait of Hormuz da jirgin soji zai iya haifar da farmaki.

Dakarun juyin juya halin Iran sun yi gargaɗin kai hari ga duk wani jirgin ruwa na soja da ya yi yunƙurin bi ta mashigin Hormuz.

Kalaman sun zo ne bayan rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ta ce jiragen ruwan sojin Amurka biyu sun wuce ta mashigar, a karon farko tun bayan soma yaƙin.

Sai dai Tehran ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa ita ce ke iko da mashigar ruwan.

Tun da fari dai, Washington ta ce dakarunta sun fara cire nakiyoyi daga mashigar, ikirarin da Tehran ta sake musantawa.

Wani jami’in sojan Amurka ya ce ƙoƙarin na mayar da hankali ne kan samar da hanya mai tsaro ga jiragen kasuwanci.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments