Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta tura mutane 386 gidan yari bisa zargin aikata laifukan...

Gwamnatin Tarayya ta tura mutane 386 gidan yari bisa zargin aikata laifukan ta’addanci

Mutum 386 sun shiga gidan yari bayan Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da su kan laifukan ta’addanci.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da daure mutum 386 daga cikin mutane 508 da ake tuhuma da aikata laifukan ta’addanci, bayan wata gagarumar shari’a da aka gudanar a Abuja.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.

A cewarsa, an wanke mutum biyu daga zargin, yayin da aka sallami wasu takwas.

Sauran mutum 112 kuma za a ci gaba da shari’arsu daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Yuni.

Rahotanni sun nuna cewa an fara wannan shari’a ne tun ranar Talata a Babbar Kotun Tarayya, inda aka yanke hukunci daban-daban ga wadanda aka samu da laifi, daga daurin shekaru takwas zuwa daurin rai-da-rai, bisa la’akari da girman laifukan da suka aikata.

Ministan ya ce matakin wani sako ne ga masu aikata laifuka, yana mai jaddada cewa Najeriya ba za ta amince da ta’addanci ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments