Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan ƙaruwar sace-sacen mutane a sassan Najeriya, inda ta ce an sace mutane aƙalla 1,100 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun 2026, kuma mafi yawa a jihohin Arewa.
Amnesty International ta ce dole ne gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta gaggauta ɗaukar matakan magance wannan matsala da ke ƙara muni, musamman a tsakanin al’ummar karkara da mazauna sansanonin ƴan gudun hijira.
Malam Isa Sanusi, daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ya bayyana cewa bayan wani bincike da jami’anta suka gudanar ne ya gano yawan mutanen da aka sace, kuma sun fahinci cewa waɗanda aka yi garkuwa da su suna fuskantar nau’ikan cin zarafi sosai, ciki harda azabtarwa da horo da yunwa da fyaɗe da kuma tilasta masu aikata kisa.
Ya ce ”Mutane mafi yawa da aka sace a lokaci guda su ne a jihar Borno, a wani gari da ake cewa Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza, inda ƴan ta’adda suka sace mutane fiye da 300.
Sannan kuma akwai mutane kusan 200 da aka sace a Woro a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.”
Malam Isa Sanusi ya ƙara da cewa ”Akwai wanda kuma a jihar Zamfara aka sace mutum 150 a ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda aka ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa mata ne da yara.”