Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya raba Naira miliyan 334 ga mata 6,680 a faɗin jihar, a ƙarƙashin shirin gwamnatinsa na ƙarfafa mata da bunƙasa tattalin arziki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin raba tallafin da aka gudanar a Kano, inda ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin rage talauci, inganta rayuwar al’umma, da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa kowace daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin na karɓar Naira 50,000 a kowane wata, tare da ƙarin cewa adadin mata masu cin gajiyar shirin ya ƙaru daga 5,200 zuwa 6,680 a dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya kuma bayyana shirin a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa iyalai da kuma haɓaka harkokin tattalin arziki a matakin ƙasa, yana mai jaddada cewa ba wai tallafin kuɗi kaɗai ba ne, har ma da gina rayuwa mai ɗorewa.