Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGawuna ya gana da Kwankwaso a Abuja bayan sauya sheka

Gawuna ya gana da Kwankwaso a Abuja bayan sauya sheka

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sa labule da tsohon ɗan takarar gwamna na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a birnin Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ganawa na zuwa ne bayan sauye-sauyen siyasa da suka faru a jihar, inda Gawuna ya koma jam’iyyar ADC, yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026, Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci wata tawaga zuwa gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke unguwar Maitama a Abuja.

Sanarwar da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya fitar ta ce:

“Mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya karɓi bakuncin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna tare da Sheikh Ishaq Adam a gidansa da ke Maitama, Abuja.”

Rahoton ya nuna cewa ganawar ta gudana ne cikin yanayi na fahimtar juna, duk da sauye-sauyen da suka faru a bangaren jam’iyyun siyasa.

A halin yanzu, ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna a ganawar ba, amma ana ci gaba da sa ido kan duk wani sabon ci gaba da zai biyo baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments