Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiEFCC ta kama mutane 31 da ake zargi da karɓan horon damfara...

EFCC ta kama mutane 31 da ake zargi da karɓan horon damfara ta intanet a Abuja

Hukumar EFCC ta kama mutane 31 da ake zargi da damfara ta intanet a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026, a wata cibiyar horo da ke Becki Estate, Karu, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Hukumar EFCC ta kama mutane 31 da ake zargi da damfara ta intanet a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026, a wata cibiyar horo da ke Becki Estate, Karu, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Waɗanda aka kama sun haɗa da shugabanni biyu da kuma wasu ɗalibai masu koyon aikin damfara.

A sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce an cafke mutanen yayin da suke samun horo kan damfarar intanet.

EFCC ta kwato wayoyin hannu, kwamfutoci guda 18, da sauran na’urori daga hannunsu.

Rahotanni sun nuna cewa cibiyar na killace waɗanda ake horaswa a cikin harabar, tare da takaita motsinsu, har ma da ƙwace wayoyinsu domin katse masu hulɗa da waje.

EFCC ta ce:

“Binciken EFCC ya nuna cewa wasu daga cikin ɗaliban an yaudare su ne daga jihar Benue da alkawarin samun aiki, amma bayan sun isa cibiyar, sai aka ba su na’urorin sadarwa, kwamfutoci da manhajoji domin fara horas da su kan damfarar intanet.”

Rahotanni sun kuma bayyana cewa duk ɗalibin da ya karya ƙa’idoji na fuskantar hukuncin duka.

A cewar hukumar yaƙi da rashawa, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments