Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaINEC na yunkurin hana mu tsayar da 'yan takara a 2027 -...

INEC na yunkurin hana mu tsayar da ‘yan takara a 2027 – ADC

Jam’iyyar ADC ta yi ikirarin cewa na neman tauye mata hakkinta na tsayar da ’yan takara a zaben 2027.

Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar zaben Najeriya INEC, da shirya hanyoyin da za su hana ta tsayar da ‘yan takara a zaben 2027.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce matakan da INEC ke dauka na iya hana ta shiga zabe gaba daya, duk da cewa hukumar na cewa matakin na bin doka ne sakamakon shari’ar da ke gaban kotu.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga matakin da INEC ta dauka na kin hulda
ADC har sai an kammala shari’ar shugabancin jam’iyyar a kotun tarayya.

Sai dai ADC ta ce wannan mataki na barazana ga ikon ta na cika sharuddan doka, musamman wa’adin kwanaki 21 da dokar zabe ta tanada.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments