Jam’iyyar ADC a jihar Katsina ta nuna matuƙar damuwa da sabon jerin hare-haren ‘yan bindiga da ake kaiwa a wasu ƙauyuka, inda aka kashe jami’an tsaro da fararen hula.
Shugaban jam’iyyar na jiha, Lawal Tukur-Batagarawa, ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina, inda ya nuna damuwa kan yawaitar tashin hankali a wasu sassan jihar.
Ya ce musamman hare-haren da aka kai karamar hukuy Matazu da Musawa sun nuna cewa tsaro a jihar na ƙara lalacewa, abin da ke buƙatar daukar mataki nan da nan.
Tukur-Batagarawa ya ƙara da cewa hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ciki har da ‘yan sanda da mazauna ƙauyuka, sannan an lalata gidaje da dukiyoyi da yawa.
Ya ce duk da cewa an riga an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa, hakan bai hana tashin hankali ba, wanda ke jefa tambaya kan inganci da dorewar irin waɗannan yarjejeniyoyi.
Shugaban jam’iyyar ya danganta rashin tsaron da ake fama da shi ga rashin jagoranci mai kyau da kuma gazawar hukumomi wajen samar da isasshen tsaro ga jama’a.
Ya ƙara da cewa:
“Babban aikin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin mutane, kuma wannan ba za a yi wasa da shi ba.”
ADC ta mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa da al’ummomin da aka kai hare-haren, tare da yin kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakai masu ƙarfi da gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.