Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta nesanta kanta daga yarjejeniyar sauya filin Kwalejin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Kano ta nesanta kanta daga yarjejeniyar sauya filin Kwalejin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a duk wani shiri na musayar filin Kwalejin Tarayya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, Mustapha Muhammad ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da duk wani shiri ko tattaunawa dangane da filin makarantar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwalejin ta FGC dake Kano tana ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya ne ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa, wadda ita ce ke da alhakin yanke duk wani hukunci da ya shafi makarantar, tare da yin watsi da duk wani yunƙuri na danganta gwamnatin Kano a matsayin marasa tushe balle makama.

Gwamnatin dai ta kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai, da su dinga tabbatar da sahihancin labarai kafin wallafawa, tare da bin ƙa’idojin aikin jarida.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments