Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBayan shekaru 10 da gina biranen Kwankwasiyya, Amana , da Bandarawo, har...

Bayan shekaru 10 da gina biranen Kwankwasiyya, Amana , da Bandarawo, har yanzu babu mazauna sosai

Gwamnatin Jihar Kano ta kirkiro shirin gina manyan birane guda uku tun a shekarar 2012 domin rage cunkoso a Kano tare da mayar da ita birni na zamani. An gina gidaje kusan 1,500 a biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo.

Gwamnatin Jihar Kano ta kirkiro shirin gina manyan birane guda uku tun a shekarar 2012 domin rage cunkoso a Kano tare da mayar da ita birni na zamani. An gina gidaje kusan 1,500 a biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo.

A Kwankwasiyya kadai, an gina gidaje kimanin 500 zuwa shekarar 2015 domin magance matsalar gidaje da cunkoso. Sai dai bayan fiye da shekaru 10 da kaddamar da birnin, har yanzu gidaje da dama ba a zauna a ciki ba duk da kashe sama da Naira biliyan 35.

An tsara birnin da muhimman abubuwa kamar asibiti, makarantu, kasuwanni, otal-otal, masallatai da wuraren shakatawa, amma mutane kalilan ne suka tare a cikinsa tare da iyalansu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadi kan yadda gidajen ba su cika da mazauna ba bayan ya ziyarci wurin, inda ya dauki matakai kamar gudanar da tarukan majalisar gwamnati a wurin domin karfafa mutane su zauna a birnin.

Rahotanni sun nuna cewa matsalolin tsaro da rashin wadataccen ruwa na daga cikin manyan dalilan da suka hana mutane komawa, duk da cewa gwamnati ta samar da wutar lantarki ta hanyar tashar Tiga.

Haka kuma, wasu ma’aikatan gwamnati sun ce gidajen sun fi karfin masu karamin karfi, domin yawancinsu sun tafi hannun ‘yan siyasa da manyan jami’ai, wanda ya sa ba su cika zama a ciki ba.

Wasu sun ce da an bai wa ma’aikata dama, da an samu cikakken zama a gidajen, amma tsadar su ya sa mutane da dama ba za su iya saya ba.

Sai dai gwamnatin ta ce an bai wa wasu rangwame ga manyan ma’aikata, amma da dama ba su iya saya ba, wanda ya sa aka sayar da gidajen ga masu hali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments