Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta ƙasa FRSC ta sauya wurin aiki ga jami’ai 162, tare da nada sabon mai magana da yawunta.
Babban Kwamandan hukumar, Malam Shehu Mohammed, ya amince da sauya wurin aiki ga manyan jami’ai 162 a wani babban sauyi a cikin shugabancin hukumar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamanda ACC mai kula da harkokin gudanarwa a Sashen Ilimantar da Jama’a na Hukumar CPEO, Mista Agboola Olundegun, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Mohammed ya ce wannan sauyi na da nufin karfafa ayyukan hukumar da inganta tsaron hanyoyi a fadin kasar.
Ya ce sauyin ya hada da nada sabbin shugabannin yankuna hudu wato Zonal Commanding Officers da kuma sauya wurin aiki ga kwamandojin jihohi zuwa muhimman wurare a fadin kasar.
Haka kuma, ya amince da nada sabon shugaban sashen yada labarai CPEO, inda aka daga mukamin tsohon mataimaki wato DCPEO, DCC Osondu Ohaeri, domin jagorantar dabarun sadarwa na hukumar.
Jihohin da sauyin ya shafa sun hada da Babban Birnin Tarayya Abuja, Rivers, Kaduna, Bauchi, Imo, Benue, Yobe, Ogun, Delta, Osun, Kogi, Bayelsa da Akwa Ibom.
Sabbin shugabannin yankuna sun hada da ACM C.Z. Mathew a Benin, ACM A.L.O. Ruk a Enugu, ACM B.S. Akande a Sokoto da ACM Leye Adegboyega a Bauchi.
Haka kuma, an sauya wurin aiki ga wasu kwamandoji zuwa jihohi daban-daban domin karfafa ayyuka a filin aiki.
Mohammed ya ce an yi wadannan nadin ne bisa kwarewa, gogewa da bukatun aikin kasa, yana mai jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da tura kwararrunta zuwa wuraren da za su fi bada gudunmawa.
Ya kuma bukaci sabbin jami’an da aka nada da su nuna kwarewa, sadaukarwa da kyakkyawan shugabanci a ayyukansu, tare da jaddada manufar hukumar ta rashin juriya ga take dokokin hanya da hadurran da za a iya kauce musu.