Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeKasashen Musulmi sun yi Allah-wadai da Isra’ila kan dokar hukuncin kisa

Kasashen Musulmi sun yi Allah-wadai da Isra’ila kan dokar hukuncin kisa

Kasashen Musulmi da suka hada da Saudiyya, Turkiyya da Indonesiya sun yi Allah-wadai da amincewa da wata doka a Isra’ila da ke tanadar hukuncin kisa ga Falasdinawa a yankin West Bank da aka mamaye, suna mai cewa hakan na barazana ga zaman lafiyar yankin.

Kasashen Musulmi da suka hada da Saudiyya, Turkiyya da Indonesiya sun yi Allah-wadai da amincewa da wata doka a Isra’ila da ke tanadar hukuncin kisa ga Falasdinawa a yankin West Bank da aka mamaye, suna mai cewa hakan na barazana ga zaman lafiyar yankin.

Ministocin harkokin wajen kasashen Saudiyya, Masar, Jordan, Indonesiya, Pakistan, Qatar, Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka fitar da sanarwar hadin gwiwa.

Sanarwar ta bayyana dokar a matsayin wani mataki mai hadari, musamman saboda ana zargin tana wariya ga fursunonin Falasdinawa, tare da gargadin cewa hakan na iya kara tayar da hankali da rikici a yankin.

A karkashin dokar da majalisar Isra’ila ta amince da ita, Falasdinawan da kotunan soja suka samu da laifin kai hare-haren da suka yi sanadin mutuwa, za su fuskanci hukuncin kisa.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun soki dokar, yayin da Amurka ta bayyana goyon bayanta ga ‘yancin Isra’ila na kafa dokokinta.

Yawancin kasashen da suka soki dokar suna aiwatar da hukuncin kisa a kasashensu, ciki har da Saudiyya wadda ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 356 a shekarar 2025.
Sabuwar dokar ta samar da tsarin shari’a mai tsauri ga Falasdinawa, domin ana gurfanar da su ne a kotunan soja, sabanin kotunan farar hula na Isra’ila da ke iya zartar da hukuncin daurin rai da rai ko kisa.

Isra’ila ta taba aiwatar da hukuncin kisa sau biyu kacal a tarihinta: a 1948 kan wani jami’in soja da aka samu da cin amanar kasa, sannan a 1962 kan dan Nazi Adolf Eichmann.

Isra’ila na ta mamaye yankin West Bank tun shekarar 1967, kuma tashin hankali a yankin na ta ƙaruwa tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoban 2023 wanda ya haddasa yakin Gaza.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments