Jam’iyyar ADC ta zargi INEC da nuna halin rashin adalci, tana mai cewa tana karya doka tare da nuna bangaranci a rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.
Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya yi wannan zargi a ranar Alhamis yayin da yake magana a shirin Morning Show na tashar Arise Television.
Abdullahi ya bayyana cewa tsohon jami’in jam’iyyar, Nafiu Bala Gombe, ba shi da hurumin doka na ci gaba da wakiltar jam’iyyar, yana mai jaddada cewa wa’adinsa ya kare tun bayan da ya yi murabus tare da rushe kwamitin zartarwa da yake ciki.
Ya kuma kara da cewa Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC), wanda shi ne mataki na gaba bayan babban taron jam’iyya, ya riga ya dauki muhimman matakai da suka zama wajibi ga tsarin shugabancin jam’iyyar.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya kuma kalubalanci matakan da INEC ke dauka, inda ya zarge ta da ci gaba da amincewa da wasu matakai da Bala ke yi duk da cewa tana da masaniyar cewa ya yi murabus, lamarin da ya nuna cewa hukumar na nuna bangaranci a rikicin cikin gida na jam’iyyar.