Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYadda jigo a APC daga Kano ya mutu a otal gabanin taron...

Yadda jigo a APC daga Kano ya mutu a otal gabanin taron jam’iyyar na ƙasa

Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulsalami Ginsau, ya rasu a otal din Chida da ke yankin Utako a Abuja.

Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulsalami Ginsau, ya rasu a otal din Chida da ke yankin Utako a Abuja.

Marigayin, wanda lauya ne, shi ne shugaban kwamitin da aka dora wa alhakin shirya masaukin wakilan Kano zuwa babban taron APC da aka kammala kwanan nan. An ce ya rasu ne ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026 bayan da aka yi zargin ya makale wa a cikin lifta da ta lalace a otel din.

Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce Ginsau ya je Abuja tun kafin taron domin shirya masauki. Bayan ya kammala aikin, ya sauka a otel din Chida. Sun fara zargin wani abu ba daidai ba ne lokacin da ba su gan shi a wurin taron ba, wanda ya sa suka fara nemansa a ko’ina cikin Abuja.

Rahoton Daily Trust ya ce sun kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Utako, inda aka sanar da su cewa an samu wani lamari a otel din Chida. Da suka je otel din, sun gano gawar tasa ce. Ya dora alhakin lamarin kan sakacin gudanarwar otel din, yana mai cewa an riga an yi korafi kan lalacewar liftar tasu.

An kai gawar marigayin dakin gwaje-gwaje, kuma ana jiran sakamakon binciken ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa an kai rahoton lamarin, kuma ana ci gaba da bincike.

Wata majiya daga otel din ta ce an yi wa wakilan APC daga Kano rajistar dakuna 150, amma sama da mutane 1,000 ne suka hallara, wanda ya haddasa cunkoso. Ta ce daya daga cikin liftocin su ya lalace kuma aka bude shi da karfi. Marigayin ya shiga liftar da ta lalace da asubahin ranar Juma’a, inda liftar ta fadi da shi ba tare da sanin ma’aikatan otel ba.

An ce washegari ne aka fara jin wari a otel din, wanda ya sa aka fara bincike har aka gano gawarsa.

A halin yanzu, APC da iyalan marigayin sun bukaci cikakken bincike kan lamarin. Jam’iyyar ta kafa kwamitin bincike tare da hukumomin tsaro, yayin da gwamnatin Jihar Kano ta yi alkawarin gano hakikanin abin da ya faru.

Iyalan marigayin sun bayyana mutuwar tasa a matsayin abin firgici, suna mai cewa yana cikin koshin lafiya kafin tafiyarsa.
Za a yi jana’izarsa a Kano ranar Alhamis bisa tsarin addinin Musulunci.

Ginsau fitaccen lauya ne kuma jigo a APC, wanda ya yi aiki a fannoni da dama na shari’a da harkokin kasuwanci. Ya yi karatu a Jami’ar Musulunci da ke Uganda da kuma Makarantar Shari’a ta Najeriya a Abuja. Ya bar mata biyu da ’ya’ya biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments