Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiCikin jarirai biyar da aka haifi, daya ta rasu, hudu na samun...

Cikin jarirai biyar da aka haifi, daya ta rasu, hudu na samun kulawa a ICU

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar daya daga cikin jarirai biyar, yayin da hudu ke ci gaba da jinya a ICU.

Ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a ranar laraba ta rasu, yayin da sauran huɗu ke ci gaba da karɓar kulawa ta musamman a asibiti, bayan haihuwarsu kafin cikar lokaci.

‎Jami’an asibitin sun tabbatar da rasuwar jaririyar a ranar Lahadi, sakamakon matsalar numfashi (apnoea) da ta janyo tabarbarewar lafiyarta, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceton rayuwarta ta hanyar ƙarin jini. Rahotanni sun nuna cewa jaririyar na da nauyin kilo 1.3 a lokacin rasuwarta.

‎Sauran jarirai huɗun na cikin mawuyacin hali, inda ake kula da su a sashen kulawa ta musamman ga marasa lafiya masu tsananin buƙata.

‎Mai magana da yawun Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta bayyana cewa an haifi jariran ne ba su kai cikakken lokacin haihuwa ba, lamarin da ya sa aka garzaya da su kai tsaye zuwa sashen kulawa ta musamman domin ceton rayukansu.

‎Ta ce ana kula da su ne saboda ƙarancin nauyin jikinsu da kuma haɗarin kamuwa da cututtuka, ciki har da kamuwa da ƙwayoyin cuta, rawayar jiki (jaundice), da kuma matsalolin daidaita zafin jiki da sukari a jini.

‎A wani ɓangare mai tayar da hankali kuwa, rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar jariran ta rasu a daren Laraba sakamakon zubar jini mai tsanani bayan haihuwa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments