Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce ta tsawaita wa’adin yi wa ƴaƴan jam’iyyu rajista yayin da zaɓen shekara mai zuwa na 2027 ke ci gaba da ƙaratowa.
INEC ta ce maimakon wa’adin farko da ta bayar na 21 ga watan Afirilun 2026, yanzu an mayar da shi zuwa 10 ga watan Mayun, 2026 matsayin ranar ƙarshe ta karbar rajistar ƴaƴan jam’iyyun Najeriya.
Sai dai an buƙaci jam’iyyun da kar su wuce mako uku wato kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓe fitar da ƴan takara.
Mai magana da yawun hukumar zaɓen, Zainab Aminu ta ce hukumar zaben ta fitar da sabon jadawalin ne bayan ƙorafi ko jan hankali da jam’iyyun siyasar ƙasar suka gabatar wa da INEC ɗin, shi ne ya sa suka ɗauki wannan mataki.
“Dogaro da sashen sabuwar dokar zaɓen 2026 sashe na 77 sakin layi na huɗu da ya buƙaci dukkan jam’iyyu su gabatar da rajistar ƴan jam’iyyarsu kwanaki 11 kafin gudanar da zaɓukan cikin gida, shi ya sa aka samar da wannan sauyi”, in ji Zainab Aminu.
Hukumar zaɓen ta tsayar da 23 ga watan Afirilun zuwa 30 ga watan Mayun, 2026, wanda hakan ba ya rasa nasaba da dalilan da suka sa INEC sake tsawaita wa’adin zuwa 10 ga watan Mayun wajen karɓar rajistar.
Haka kuma ta ce akwai hukumce-hukumce da dokar zaben ta tanada, kan dukkan waɗanda suka gaza gabatar da rajistar ƴan jam’iyyar tasu a kan lokaci.
”Ita hukumar zaɓe na amfani ne da dokoki na zaɓe, da kuma na ƙasa da tanade-tanaden zaɓe, idan har kuma aka ce akwai doka to saba mata akwai hukunci da aka tanada”