Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kano ya taya Tinubu murnar cika shekaru 74 da haihuwa

Gwamnan Kano ya taya Tinubu murnar cika shekaru 74 da haihuwa

Gwamnan Kano ya yi wa Shugaban ƙasa Tinubu fatan alheri yayin da yake cika shekaru 74 da haihuwa.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da saƙon taya murna ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 74.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu.

Gwamnan ya bayyana ranar haihuwar Shugaban a matsayin wata dama ta yabawa shugabancin sa, jajircewarsa da kuma ƙoƙarinsa wajen hidimtawa ƙasa.

Gwamnan ya kuma yaba da irin hangen nesa da ƙoƙarin da shugaban ƙasar yake dashi musamman a fannin ƙarfafa haɗin kan Najeriya, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Daga bisani gwamna Abba na yabawa manufofin gwamnatin ta shugaba Tinubu na Renewed Hope Agenda wanda ke da manufar ci gaba da ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments