Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiTinubu ya bada kariya ga gyaran dokar zaɓe daga sukar ƴan adawa.

Tinubu ya bada kariya ga gyaran dokar zaɓe daga sukar ƴan adawa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce sukar da jam’iyyun adawa ke yi ga sabuwar dokar zaɓe ta 2026 ba su yin amfani ga al’ummar Najeriya. Ya bayyana cewa an bi dukkan matakan doka wajen amincewa da dokar, kuma manufarta ita ce ƙarfafa tsarin zaɓe da demokuraɗiyya.

Ya kuma ƙaryata zargin cewa jam’iyyar APC na son mayar da ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa dimokuraɗiyya na buƙatar adawa mai ƙarfi.

Tinubu ya ce duk da matsalolin tattalin arziki na duniya, gwamnatinsa ta samu ci gaba a fannoni kamar hanyoyi, gyaran haraji, da jawo zuba jari, tare da alƙawarin inganta wutar lantarki.

Ya kuma jaddada muhimmancin bai wa matasa da mata dama a harkokin siyasa, yana mai cewa haɗin kai ne ginshiƙin cigaban ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments