Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGabanin sauya sheƙarsa zuwa ADC, Kwankwaso ya gana da Atiku

Gabanin sauya sheƙarsa zuwa ADC, Kwankwaso ya gana da Atiku

Kafin komawarsa ADC, Kwankwaso ya yi wata ganawa da Atiku.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, gabanin hasashen sauya sheƙar Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC.

A wani saƙo da ya wallafa, Atiku ya ce: “Yau da yamma na karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, a wata ziyarar girmamawa.

Mun yi tattaunawa mai zurfi kan halin da ƙasa ke ciki.”

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin sauya sheƙar Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments