Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSojoji sun kashe ‘yan ta’adda 38 a Borno.

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 38 a Borno.

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI, sun sanar da kashe aƙalla ‘yan ta’adda 38 da ake zargin na ISWAP ne, bayan sun kai hari wani sansanin soji da ke ƙauyen Mandaragirau a ƙaramar hukumar Biu, jihar Borno da safiyar Asabar.

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI, sun sanar da kashe aƙalla ‘yan ta’adda 38 da ake zargin na ISWAP ne, bayan sun kai hari wani sansanin soji da ke ƙauyen Mandaragirau a ƙaramar hukumar Biu, jihar Borno da safiyar Asabar.

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce sojojin sun fatattaki harin da ‘yan ta’addan suka kai daga bangarori da dama, inda suka tilasta musu janyewa cikin ruɗani bayan sun fuskanci tsayayyen martani daga sojoji.

Ya kuma bayyana cewa rundunar sojin sama ta bayar da taimako ta sama, tare da samar da bayanan leƙen asiri domin ƙara inganta kai hare-hare kan ‘yan ta’addan.

A cewarsa, bayan bin sawun ‘yan ta’addan yayin da suke guduwa, an ƙara kashe da dama daga cikinsu. Jimillar kusan 38 aka hallaka, inda aka gano gawarwaki 8 a wajen artabun, yayin da rahotanni daga 6mazauna yankin suka nuna akwai sama da 30 da suka mutu a hanyar Garin Mallum zuwa Garin Gajere har zuwa yankin Timbuktu Triangle.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi guda 7, bama-baman RPG guda 4 da sauran harsasai. Ba a samu asarar rai a ɓangaren sojoji ba, sai dai wata mota kirar MRAP ta samu rauni sakamakon harin RPG, yayin da aka ba waɗanda suka ji rauni kulawar gaggawa.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike a yankunan domin ƙara gano gawarwaki da kuma tabbatar da nasarar da aka samu, tare da yabawa sojojin bisa jarumtaka da ƙarfinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments