Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLabaraiJa’oji ya yi murabus daga mukamin da Tinubu ya bashi, gabanin zaɓen...

Ja’oji ya yi murabus daga mukamin da Tinubu ya bashi, gabanin zaɓen 2027.

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan harkokin zama ɗan ƙasa da shugabanci, Nasir Bala Aminu, wanda aka fi sani da Ja’oji, ya yi murabus daga mukaminsa gabanin zaɓen 2027.

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan harkokin zama ɗan ƙasa da shugabanci, Nasir Bala Aminu, wanda aka fi sani da Ja’oji, ya yi murabus daga mukaminsa gabanin zaɓen 2027.

Murabus ɗin ya biyo bayan umarnin Bola Ahmed Tinubu wanda ya buƙaci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara su sauka daga mukamansu kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.

Wannan umarni ya shafi ministoci, masu ba shugaban ƙasa shawara, manyan mataimaka na musamman da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin yanzu.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Ja’oji ya gode wa shugaban ƙasa bisa damar da aka ba shi na yi wa ƙasa hidima, yana mai cewa nadin nasa alama ce ta yadda gwamnati ke ƙarfafa matasa.

Ya kuma bayyana cewa amincewar da aka ba shi na riƙe mukamai muhimmai ya samo asali ne daga yadda shugaban ƙasa ke da imani da matasa da kuma burinsa na ba su dama su taimaka wajen cigaban ƙasa.

Ja’oji ya ƙara da cewa har yanzu yana da biyayya ga gwamnati kuma a shirye yake ya ci gaba da yi wa ƙasa hidima a duk lokacin da aka buƙace shi a gaba.

Haka kuma, ya yaba da shirin “Renewed Hope Initiative” na gwamnati, yana mai cewa yana taimakawa wajen inganta manufofi da shirye-shiryen cigaban ƙasa.

Ya yi fatan cewa idan aka ba gwamnati wani zangon mulki bayan 2027, za a samu ƙarin nasarori daga manufofin da aka fara.

Ana kallon murabus ɗinsa a matsayin alamar cewa yana shirin tsayawa takara, kodayake bai bayyana kujerar da yake nema ba. Sai dai rahotanni sun nuna cewa yana da niyyar tsayawa takarar wakilin mazabar Tarauni a Majalisar Wakilai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments