Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikata su yi aiki daga gida saboda babban...

Gwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikata su yi aiki daga gida saboda babban taron APC

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ma’aikatan da ke aiki a Sakatariyar Tarayya a Abuja za su yi aiki daga gida a ranar Juma’a.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci ma’aikatan gwamnati da ke aiki a Babban Sakatariyar Tarayya da ke Abuja su yi aiki daga gida a ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026.

An fitar da wannan umarni ne a wata takarda da aka saki ranar Alhamis, wacce Abdul Garba, babban sakataren sashen jin D’daɗin M’ma’aikata ya sanya wa hannu a madadin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A cewar takardar, za a rufe duk hanyoyin shiga da kewayen sakatariyar gwamnatin tarayya mataki na 1, 2 da 3, daga ranar Juma’a 27 zuwa Asabar 28 ga Maris, 2026.

Gwamnatin ta ce an ɗauki wannan mataki ne saboda za a yi amfani da Eagle Square domin gudanar da babban taron jam’iyyar APC a waɗannan kwanaki.

Haka kuma, an umarci dukkan ma’aikatan ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati da ke cikin wuraren da abin ya shafa, har da ma’aikatar harkokin waje, da su yi aiki daga gida a ranar Juma’a.

Gwamnatin ta kuma buƙaci shugabannin ma’aikatu da hukumomi su tabbatar da cewa an bi wannan umarni yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments