Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFiye da daliget 8,000 tare da gwamnonin 31 za su kasance a...

Fiye da daliget 8,000 tare da gwamnonin 31 za su kasance a babban taron APC

Babban taron APC na ƙasa zai samu halartar daliget 8,000 da gwamnonin jihohi 31.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa wakilai sama da 8,433 ne ake sa ran za su halarci babban taronta na kasa da za a gudanar an Eagle Square.

Ana sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnoni 31 da ministoci, za su jagoranci mahalarta taron.

Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai an Abuja, inda ya ce an kammala shirye-shirye domin gudanar da taron cikin nasara.

Ya ce taron, wanda za a yi daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Maris, zai ba jam’iyyar damar zaben sabbin shugabannin kasa da za su jagoranci harkokin APC gabanin zaben 2027.

A APC ta tabbatar da cewa za ta yi amfani da tsarin sasanci wajen zabar shugabanninta a wannan babban taro.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments