Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ta rasu, inda aka ce ta rasu ne da yammacin ranar Juma’a.
Hon. Bello El-Rufai, jikanta, ya tabbatar da rasuwar inda ya ce:
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Daga Allah muka fito, gare Shi kuma za mu koma. Ina sanar da jama’a rasuwar kakata, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu ‘yan sa’o’i da suka gabata.”
Ya ƙara da cewa ita ce mahaifiyar Malam Nasir El-Rufai, yana mai nuna godiya ga rayuwar da ta yi tare da addu’ar Allah ya jikanta. Ya kuma roƙi jama’a da su yi musu addu’a.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da El-Rufai ke tsare, bayan ICPC ta gurfanar da shi a gaban kotu kan zarge-zarge guda 10 da suka shafi zargin karkatar da dukiyar jama’a da kuma wanke kuɗi.
Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen, yayin da wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta ɗage sauraron neman belinsa zuwa ranar 31 ga Maris, kamar yadda mai shari’a, Rilwanu Aikawa, ya bayyana bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu.