Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiNSCDC za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa don yaƙi da...

NSCDC za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa don yaƙi da laifi.

Hukumar NSCDC ta bayyana shirin ta na amfani da jiragen sama marasa matuƙi da sauran sabbin fasahohi domin kare muhimman kayayyakin ƙasa daga masu aikata laifuka.

Hukumar NSCDC ta bayyana shirin ta na amfani da jiragen sama marasa matuƙi da sauran sabbin fasahohi domin kare muhimman kayayyakin ƙasa daga masu aikata laifuka.

Babban kwamandan hukumar, Ahmed Audi, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da kwamandojin jihohi da manyan jami’ai a hedikwatar su da ke Abuja. Ya ce hukumar na sauya tsarin yaki da laifi zuwa wanda ya fi zama na gaba-gaba.

Ya kuma jaddada muhimmancin horo da ƙwarewa, tare da cewa aiki da gaskiya da bin ƙa’idoji ba za su zama abin sassauci ba. Haka kuma ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin inganta tsaro a ƙasa.

Bayan taron, an raba kayan aiki na zamani ga kwamandojin jihohi domin ƙara inganta sa ido da saurin amsa kiran gaggawa.

Kayan sun haɗa da drones guda uku a kowace jiha, jakunkunan aiki masu ɗauke da tablets, solar chargers da GPS, sannan akwai rigunan kariya, hular kariya, takalman soja, da sauran kayan aiki.

Ahmed Audi ya gargadi cewa dole ne a yi amfani da waɗannan kayan ne kawai domin aikin hukuma, yana mai cewa duk wanda aka samu da amfani da su ba daidai ba zai fuskanci hukunci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments