Akalla sojoji 11 da jami’in ‘yan sanda guda ɗaya sun mutu bayan ‘yan bindiga sun kai musu harin kwanton ɓauna a ƙauyen Giro Masa dake ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Lamarin ya faru ne yayin da jami’an tsaro ke bin sahun ‘yan bindigar, amma aka kai musu hari a hanya tare da ƙone motocin soja guda biyu.
Gwamnan jihar, Nasir Idris, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai alƙawarin tallafa wa waɗanda s jiuka jikkata da iyalan mamatan.
Mazauna yankin sun ce ƙungiyar Lakurawa na yawan kai hare-hare, kuma wannan lamari ya ƙara jefa su cikin tsoro. Sun buƙaci gwamnati ta ƙara tura jami’an tsaro domin kare rayukansu.
A gefe guda, an ruwaito cewa a cikin watanni uku kacal, sama da sojoji 50 sun mutu a hare-hare a Borno da Adamawa.
A tattaunawar da Dakta Yahuza Getso ya yi da Daily Trust, ya bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na nuna gazawa a tsarin tsaron ƙasa, yana mai jaddada bukatar inganta tattara bayanan sirri, samar da kayan aiki na zamani, da kuma ɗaukar matakin kai farmaki kan ‘yan ta’adda kafin su kai hari.